An gudanar da jana'izar shahidan Al-Hashd al-Shabi a daidai lokacin da ake cika shekaru biyu da harin da Amurka ta kai a hedkwatar dakarun Al-Hashd da ke yammacin Iraki tare da halartar dimbin jama'a.
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, a dandalin Tahrir da ke birnin, a safiyar laraba ne al'ummar kasar Iraki suka gudanar da bukukuwan cika shekaru biyu da shahadar sojoji na Al-Hashd al-Shabi wanda sojojin Amurka suka kai.
Harin wanda aka kai a ranar 29 ga watan Disamba, 2019, a yankin al-Qaim na lardin Anbar, kusa da kan iyakar Syria, a hedkwatar dakarun al-Hashd al-Shabi, ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100 tare da jikkata da dama.
A yayin taron, an zaga da hotunan jagororin gwagwarmaya, musamman Janar Qassem Soleimani da Abu Mahdi al-Mohandes da shahidan Al-Qaim, a kan motoci, kuma al'ummar Bagadaza sun yi gangami a dandalin Tahrir don nuna adawa da Amurka da laifukan da take aikatawa. suna sanar da cewa har yanzu a shirye suke su mutu, suna cikin jajircewa da bin umarnin shugabanci na malaman addini.
Da yammacin ranar 29 ga watan Disambar 2009, jiragen yakin Amurka sun kai hari kan bataliyoyin Hezbollah na Iraki da ke da alaka da al-Hashd al-Shabi a garin Al-Qaim da ke kan iyakar Syria da bama-bamai 30 da rokoki; A harin dai an kashe dakarun al-Hashd al-Shabi na Iraki 30 tare da jikkata wasu fiye da 60 na daban.
Har ila yau taro ya samu halartar kwamandojin kungiyar al-Hashd al-Shabi da suka hada da "Abu Fadak al-Muhammadawi" shugaban kwamitin al-Hashd al-Shabi da Abu al-Walai babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Islama na bataliya sayyidush shuhada As.